← All news
Press Release3 September 2026

HON. MASUD MUSA BASHAR YA TAYA SANATA ABDULAZIZ YARI, MARAFAN SOKOTO, MURNAR NADINSA A MATSAYIN DIRECTOR-GENERAL OF THE CAMPAIGN

HON. MASUD MUSA BASHAR YA TAYA SANATA ABDULAZIZ YARI, MARAFAN SOKOTO, MURNAR NADINSA A MATSAYIN DIRECTOR-GENERAL OF THE CAMPAIGN

A madadin kansa da gaba dayan shugabannin City Boy Movement a Jihar Sokoto, State Director, Alhaji Hon. Masud Musa Bashar (Turakin Wazirin Sokoto), ya taya His Excellency, Sanata Abdulaziz Yari, Marafan Sokoto, murnar nadin da aka yi masa a matsayin Director-General of the Campaign na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.

A cikin sakon taya murna, Turakin Wazirin Sokoto ya ce wannan nadin shaida ne ta musamman ga jagoranci, aminci, sadaukarwa da kwarewar siyasa da Marafan Sokoto ya nuna tsawon shekaru.

Ya nuna cikakken tabbaci cewa a karkashin jagorancinsa, wannan aiki zai kai ga nasara mai ƙarfi ga Shugaban Kasa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

City Boys Movement — Sokoto State Chapter

Signed: Hon. Ma’sud Musa Bashar Rahamaniyya, Turakin Wazirin Sokoto, State Director.

More news