← All news
Press Release3 September 2026

HON. MASUD MUSA BASHAR (TURAKIN WAZIRIN SOKOTO) YA TAYA MATAIMAKIN SHUGABAN KASA, SANATA KASHIM SHETTIMA, GCON, MURNAR CIKA SHEKARU 60

HON. MASUD MUSA BASHAR (TURAKIN WAZIRIN SOKOTO) YA TAYA MATAIMAKIN SHUGABAN KASA, SANATA KASHIM SHETTIMA, GCON, MURNAR CIKA SHEKARU 60

State Director na City Boy Movement a Jihar Sokoto, Hon. Masud Musa Bashar (Turakin Wazirin Sokoto), ya taya His Excellency, Sanata Kashim Shettima, GCON, Mataimakin Shugaban Tarayyar Najeriya, murnar cika shekaru 60 da haihuwa.

A cikin sakon taya murna, Turakin Wazirin Sokoto ya yaba da rayuwar Mataimakin Shugaban Kasa a matsayin misali na hidima, jagoranci, jajircewa, hikima da sadaukarwa ga Najeriya. Ya kuma yaba da goyon bayan da yake bayarwa ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.

Ya yi addu’ar da Allah Ya kara wa Mataimakin Shugaban Kasa rai, lafiya, ƙarfi, zaman lafiya da nasara a hidimar ƙasa.

City Boys Movement — Sokoto State Chapter

Signed: Hon. Ma’sud Musa Bashar Rahamaniyya, Turakin Wazirin Sokoto, State Director.

More news